[go: up one dir, main page]

Yadda za ka rufe asusun ka

Za ka ɗauki hutu daga X? Mun gane. Wani lokaci yana da kyau a ɗauki mataki baya daga duk abin da ke faruwa. Ko kuma idan kana neman hutu na dindindin, mu ma za mu iya taimaka maka. Bi umarnin mataki-mataki kan yadda ake rufe-ko goge-asusunka naX.

Rubutu: Idan kuna da matsalar asusu (misali. rasa postsmai bi da ba daidai ba ko ƙidayar bisaƙonnin Kai tsaye da ake zargi ko alamun karya garkuwar asusu), rufewa da sake buɗe asusunka ba zai warware shi ba. Koma ga maƙalolinmu na gano matsala ko a tuntuɓi Tallafin X.

 

Rufewa da goge asusun ka naTwitter

Rufe asusunka na Twitter shine matakin farko na goge asusunka na dindindin. Rufewa yana ɗaukar kwanaki 30. Idan ba ka shiga asusunka a cikin lokacin rufewa na kwanaki 30 ba, an goge asusunka kuma ba za a ƙara haɗa sunan mai amfani da asusunka ba.
 

 

Ana rufe asusunka na Twitter

Rufewa yana fara aikin goge asusun Twitter ɗinka na dindindin. Wannan matakin yana ƙaddamar da taga na kwanaki 30 wanda zai ba ku sarari don yanke shawara idan kuna so rsake buɗe asusunku.

Buɗe asusunka na Twitter yana nufin ba za a iya ganin sunan mai amfani (ko "hannu") da furofayil na bainar jama'a akan twitter.com, Twitter don iOS ko Twitter don Android ba. 
 

 

Ana goge asusunka na Twitter

Bayan sararin rufewa na kwanaki 30, ana goge asusunka na Twitter na dindindin. Lokacin da ba ka shiga cikin asusunka ba a cikin lokacin na kwanaki 30, yana ba mu damar sanin kana son goge asusunka na Twitter na dindindin. Da zarar an goge asusun ka, ba a samun asusun ka a cikin na'urorinmu. Ba za ka iya sake buɗe asusunka na baya ba kuma ba za ku sami damar zuwa kowane tsofaffin Tweets ba.

Da zarar an goge asusun ka bayan sararin rufewa na kwanaki 30, sunan mai amfani ɗin ka zai kasance don yin rajista ta wasu asusun Twitter.

 

Manyan abubuwan da ya kamata ka sani kafin rufe asusun ka

Ga 'yan abubuwan da za ka tuna idan ka yanke shawarar rufe ko goge asusun ka na Twitter:

  • Goge asusunka na Twitter ba zai goge bayananka daga injinan bincike kamar Google ko Bing ba saboda Twitter ba ya sarrafa waɗannan shafukan yanar-gizon. Akwai matakan da za ka iya ɗauka idan ka tuntubi injin bincike.
  • Lokacin da ka rufe asusunka na Twitter, ambaton sunan mai amfani na asusunka a cikin wasu Tweets ɗin zai kasance har yanzu. Duk da haka ba za ta ƙara haɗawa zuwa Furofayil ɗin ka ba saboda furofayil ɗin ka ba zai ƙara samuwa ba. Idan kana son a sake duba bayanan a ƙarƙashin Dokokin Twitter, kana iya shigar da tikiti a nan.
  • Ba sai ka goge asusunka ba canza sunan mai amfani ko imell masu alaƙa da asusunka na Twitter. Je ka Bayanin asusu don sabunta wancan kowane lokaci.
  • Shiga cikin asusun ka ta cikin sarari na rufewa cikin kwanaki 30 zai maido da asusunka cikin sauƙi.
  • Idan kana son sauke bayananka na Twitter, za ka buƙaci ka neme shi kafin ya rufe . Rufe asusunka baya cire bayanai daga tsarin Twitter.
  • Twitter na iya riƙe wasu bayanai akan asusun da aka rufe don tabbatar da tsaro na dandamali da mutanen da su ke amfani da shi. Ana iya samun ƙarin bayani a nan.
     

Idan kana fuskantar matsala wajen sarrafa asusunka na Twitter, duba waɗannan shawarwari don sarrafa al'amuran gama gari kafin zaɓin rufe asusun ka naTwitter.

 
Yadda za ka rufe asusun ka
Step 1

Shafa alama ta mazaɓar kewayawa , sannan ka shafa Saituna da tsare sirri.

Step 2

Shafa Asusunka, sannan ka shafa Rufe asusun ka.

Step 3

Karanta bayanan rufe asusu, sannan ka shafa Rufe.  

Step 4

Shigar da kalmar-shiga lokacin da aka tambaye ka sannan ka shafaRufe.

Step 5

Tabbatar cewa kana son ci gaba ta hanyar shafa E, a rufe.

Step 1

A cikin mazaɓar sama, ko dai za ka ga alamar mazaɓar kewayawa  ko alamar furofayil ɗinka. Shafa kowace alama da ka ke da ita, sannan ka shafa Saituna da tsare sirri.

Step 2

Shafa Asusu, sannan ka shafa Rufe asusun ka.

Step 3

Karanta bayanan rufe asusu, sannan ka shafa Rufe.  

Step 4

Shigar da kalmar-shiga lokacin da aka tambaye ka sannan ka shafaRufe.

Step 5

Tabbatar cewa kana son ci gaba ta hanyar shafa E, a rufe.

Step 1

Danna kan alamar Ƙari  sannan ka danna kan Saituna da tsare sirri daga mazaɓa mai saukewa.

Step 2

Daga madannin Asusunka, danna kan Goge Asusunka.

Step 3

Karanta bayanan rufe asusu, sannan danna Rufe

Step 4

Shigar da kalmar-shigarka lokacin da aka tambaya kuma ka tabbatar da cewa kana son ci gaba ta hanyar danna madannin rufe asusu.


Idan ka ga kana kewar X kuma bai wuce kwanaki 30 ba, shiga kawai ka bi waɗannan matakai don sake buɗe asusunka.
 

 

Rijista ta biyan kuɗi da rufe asusu 

Rufe asusunka na X ba ya soke rijistar X kai tsaye. Idan kana da duk wani biyan kuɗi mai aiki (misali X Blue, Manyan Bi) da aka saya ta manhajar X, za su ci gaba da aiki. Kana iya sarrafa waɗannan rijistar ta hanyar dandamalin da ka fara yin rijista. Rijistar da aka saya akan X.com zai soke da kansa bayan ka rufe asusun ka.

Yadda ake soke rijistar X Blue

Yadda ake soke biyan kuɗi na Super Follows

 

FAQs na Rufewa

Shin rufe Twitter shi ma yana goge saƙo na kai tsaye?

A lokacin rufewa na kwanaki 30, saƙon na Kai tsaye ba za a goge su ba Lokacin rufewa ya ƙare kuma an goge asusun ku, saƙo Kai tsaye da kuka aika kuma za a goge su.

Na rufe asusuna, amma me ya sa yake ci gaba da sake buɗewa?

Idan ka ba da izini ga duk wasu manhajojin ɓangare na daban don shiga asusun ka, wataƙila kana shiga a kaikaice daga wata manhajar. Domin shiga cikin Twitter yana sake buɗe asusun ka ta atomatik, tabbatar ka soke damar manhajar ɓangare na daban ta shiga asusunka na Twitter.

Me zai faru idan ba ni da kalmar-shiga ta lokacin da na yi ƙoƙarin rufewa?

Idan ba ka da ita a hannu, ko kana karɓar saƙon cewa ba daidai ba ce, wataƙila ka buƙaci sake saita kalmar-shigarka. Gwada neman imel ɗin sake saitin kalmar-shiga.

Na nemi imel ɗin sake saitin kalmar-shiga, amma idan na rasa damar yin amfani da adireshin imel ɗin da na saba saita asusuna fa?

Idan ka rasa damar yin amfani da adireshinka na imel wanda ke da alaƙa da asusunka na Twitter, za ka buƙaci tuntuɓar kamfanin da ke samar maka da sadarwar imel. Sami taimako don shiga adireshinka na imel. Rufewa wani mataki ne da ya zama dole mai riƙe da asusun da aka tabbatar ya ɗauka ko kuma ta buƙatar tabbataccen mai riƙe da asusu. Sai dai idan za ka iya tuntuɓar mu daga adireshin imel ɗin da aka tabbatar (ko samun damar yin amfani da lambar wayar hannu da aka tantance akan asusun), ba za mu iya rufe asusun a madadin ka ba. Idan kana da damar yin amfani da lambar wayar hannu da aka tantance akan asusunka, to za ka iya neman sake saitin kalmar-shiga.

Ta yaya zan rufe asusuna da aka kulle ko dakatarwa?

Don rufe asusun da aka dakatar ko aka kulle, miƙa buƙatar nema a nan. Haka nan ana iya tura buƙatun zuwa sunayen tuntuɓar da aka jera a ƙarƙashin "Yadda Ake Tuntuɓar Mu" na Dokar Tsare Sirrin Mu.

Hakanan za ka iya samun taimakon buɗe asusunka. Sami ƙarin bayani akan gudana da asusun ka da aka kulle ko dakatarwa, da ya haɗa da shigar da ɗaukaka ƙara.

Yaɗa wannan maƙala